Engr Muhammad Nura Khalil mutun ne da Allah ya bashi dukiya me dinbun albarka – Ibrahim Umar Kafur
Dukiyar Nur Khalil bata tsonemai ido ba domin makiyan shi da masoyan shi babu wanda baya amfana da ita.
Dan haka al’ummar jihar katsina kusani cewa Engr Muhammad Nura Khalil ba yana neman shugabancin jihar katsina bane domin ya tara dukiya, yana neman wannan kujera ne domin Allah ya taimakeshi ya gina al’ummar jihar katsina sannan kuma ya gina jihar katsina yanda za’ayi alfahari da ita a wannan kasa tamu me albarka.
Engr Muhammad Nura Khalil dan takarar gwamnan jihar katsina karkashin tutar jam’iyyar NNPP me alamar kayan mar-mari bayada wani buri face yaga jihar katsina tana tsaye da kanta ba tarika jiran sai gwamnatin tarayya ta turo mata da giran sannan tayi abinda take bukata ba.
Kirkirar wata hanya da zata kawoma jaha kudaden shugowa babban cigaba ne ga al’umma.
Allah ya kawo mana cigaba a wannan jaha tamu me albarka amin.
#NNPP2023