Sama Da Mata 7,000 Sun Mutu Wurin Haihuwa Cikin Watanni 6 A Ebonyi

Ebonyi ta sami rahoton mutuwar mata masu juna biyu 7,014 daga cibiyoyin kiwon lafiya 40 a fadin jihar tsakanin Janairu zuwa 20 ga Yuni.

Manajar shirye-shirye na jihar Ebonyi karkashin Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ga Mata da Haihuwar Yara na Hukumar Kula da Lafiya ta Amurka (USAID-IHP), Misis Augustine Otu, ta bayyana hakan a jiya yayin wani shirin horar da ma’aikatan kiwon lafiya na matakin yini daya.

Shirin da aka gudanar a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, hukumar USAID-IHP tare da sauran abokanan cigaban jihar ne suka shiryawa ma’aikatan lafiya a mako mai zuwa.

“Binciken ya nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashen da suka fi fama da matsalar mace-macen mata masu juna biyu a duniya.

Yayin da ita kuma jihar Ebonyi na daga cikin jihohin da suka bayar da gudumuwarsu a wannan matsayi.

Manajar shirin ya ce “Bincike na karshe da muka yi ya nuna mutuwar mutane 7,014 a cikin cibiyoyin lafiya 40 kacal, don haka ku yi tunanin ko mun tattara rahotanni daga wasu cibiyoyin kiwon lafiya a jihar,” in ji manajan shirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram