Sanatoci 22 na jam’iyyar APC mai mulki na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, kamar yadda tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya bayyana.
Ya bayyana cewa, an shirya sauya shekar ne saboda an hana Sanatoci tikitin takara a zaben 2023.
Da yake bayyana damuwarsa kan ficewar da aka yi a jam’iyyar, Fani-Kayode a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba ya ce dole a yi wani abu don hana afkuwar hakan.
“Sanatocin APC 22 suna barazanar sauya sheka zuwa PDP saboda an hana su tikitin komawa majalisar dattawa. Wannan yana da mahimmanci kuma dole ne a yi wani abu don hana su ficewa daga jam’iyar, Mutane da yawa sun damu kuma muna bakin kokarinmu a kowani lokaci, don tattaunawa da su, Ba za mu iya jure rasa su ba, ”kamar yadda ya wallafa.
A safiyar yau ne jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wasu Sanatoci bakwai suka fice daga APC zuwa wasu jam’iyyun adawa.
Mambobin Majalisar Dattawan da suka fice daga APC sun hada da Ibrahim Shekarau (Kano), Yahaya Abdullahi (Kebbi) Adamu Aliero (Kebbi), Dauda Jika (Bauchi), Ahmad Babba Kaita (Katsina), Lawal Yahaya Gumau (Bauchi), da Francis Alimikhena. (Edo).
Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da Sanatocin APC, Shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce abin takaici ne yadda ‘yan majalisar suke ficewa daga jam’iyyar ta APC.