Shugaba Buhari Na Bakin Ƙoƙari Wajen Magance Ƙarancin Gidaje A Najeriya – Shugaban Hukumar Gidaje

Hukumar samar da gidaje ta kasa ta ce shugaban kasa Muhammad Buhari yanzu haka nayi duk mai yiwuwa wajen magance karan gidaje ga yan Najeriya

Babban daraktan hukumar Sanata Gbenga Ashafa ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Ya kara da cewa kafin karewar wa’adin mulkin Buhari matsalar zata zama tarihi, domin kuwa kowa zai dara kan ci gaban da za a samu a bangaren.

Yayin da yake jawabi a wajen wani taron wayar da kai da aka shirya a rukunin gidajen na Lugbe, ya ce yanzu haka akwai shirye shirye da dama da aka bujiro da su, da nufin ganin an samu waraka ga matsalar.

Ya kuma ce yanzu haka akwai gidaje 300 da tuni aka kammala su a yankin Zuba, dake Abuja.

A cewar sa, gidajen an samar da su ne domin tallafawa masu kananan karfi su samu damar mallakar gidajen cikin sauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram