Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Mutane uku sun kone kurmus a ranar litinin, sanadiyyar Hatsarin mota, a Opokuma dake yamma maso gabacin hanyar koluama dake karamar Hukumar Opokuma/Koluama a jahar Bayelsa.
Jaridar Daily trust ta gano cewa, karin wasu mutane uku da suka hada da Kurtun Dan Sanda, da suka tsira da raunuka, suna cigaba da karbar magani a asibiti.
Wasu daga cikin mutanen da suka shaida lamarin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin Karfe biyar na yamma.
An cewa, motoci biyu ne Toyota Camry Mai numba LS 529 KY, da Mazda 323 Mai namba GBB 532 XA- sune suka yi karo, daya haddasa wutar.
Shaidun gani da ido,sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa, mota kirar Camry na dauke da man fetur , Wanda shine yayi sanadiyyar tashin wuta.
Mai magana da yawun Rundunar yan sandan jahar , SP Asinim Butswat, Wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa maza biyu da mace daya suka rasa rayukansu sanadiyar hatsarin, ba zasu iya ganuwa ba a dalilin konewar da suka yi.