Ƴan Bindiga Sun Sake Kai Wani Sabon Hari A Cikin Birnin Katsina

Ƴan Bindiga Sun Sake Kai Wani Sabon Hari A Cikin Birnin Katsina

Bayanai daga cikin garin Katsina sun tabbar da cewa wasu ƴan bindiga daɗi ɗauke da muggan makamai sun kai samame a wasu Unguwannin cikin birnin Katsina.

Wuraren da suka ƙaddamar da harin sun ƙunshi Sokoto Rima wajen Difiri, da bayan KTTV Inda ake kyautata zaton cewa sun Ɗauki Mutane Bakwai tare da tafiya dasu.

Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbar da kai harin, Inda ya bayyana cewa Maharan sun kai samame ne da misalin ƙarfe biyu da rabi na daren ranar 22/06/2022 ɗauke da bindigu ƙirar AK 47.

Ƴan Ta’adar sun kai hari ne a Gidan wani Ɗan Kasuwa mai suna Abdullahi Esha, a Unguwar Sokoto Rima anan Katsina sunyi awon gaba da Matar shi ƴar kimanin Shekaru Goma Sha Takwas (18).

Sai dai sashen Rundunar Ƴansandan mai kai ɗaukin gaugawa akan ayyukan Garkuwa da Mutane sun amsa kiran gaugawa, Inda suka mai da farmakin maharan tare da Kuɓutar da Yarinyar mai suna Walida Abdulaziz Maigoro, ba tare da rauni ba, a yayinda su kayi nasarar korar maharan.

Bisa ga dukkan Alamu dai ɓarayin sun dan na sunga Jini, tun suna zuwa ƙauyukan da suke zagaye da Birnin Katsina har takai ga sun fara shigowa cikin Gari, kodai Satin da ya gabata sai da Maharan suka kai wani harin tare da ɗaukar Mutane suka nemi kuɗin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram