INEC ta Ƙaryata Jita-jitar Buɗe Wurin Rajistar Katin Zaɓe A Jamhuriyar Nijar

INEC ta Ƙaryata Jita-jitar Buɗe Wurin Rajistar Katin Zaɓe A Jamhuriyar Nijar

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta musanta batun buɗe wurin rajistar Katin Zaɓe a Jamhuriyar Nijar.

Wannan cigaba na zuwa ne bayan wata jita-jita da tayi yawo a Kafafen Sadarwa na Zamani cewa Hukumar ta fara shirin yiwa ƴan Najeriya rajista baya ga cikin Ƙasa ..

Wani shafi na Facebook na wani Nche Nwabuike ya rubuta wani jawabi a ranar Laraba yana zargin INEC da buɗe wasu wuraren rajistar Katin Zaɓe a wasu Ƙasashe.

Ya rubuta “akwai wuraren rajistar Katin Zaɓe a Jamhuriyar Nijar. To yaushe ne Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ta amince a gudanar da haka a wajen Najeriya.

“Miyasa Kafafen Yaɗa Labaru na Najeriya suka yi shiru akan haka. Shin suna goyon bayan wannan shirmen? Abun kunya ga aikin Jarida.”

Duk da shafin Nnabuike na karya ne, amma jawaban shi, sun tada ƙura.

Tuni wasu suka yaɗa abinda ya faɗa, ƴan kaɗan ne suka buƙaci bayanai daga INEC, Twitter, da Facebook tana suna kira da’a ƙaryata zargin.

A lokacin da aka zanta dashi a ranar Alhamis, Kwamishinan Hukumar, Shugaban Ɓangaren Ilmin masu kaɗa ƙuri’a, Festus Okoye, wanda yace bazai ce komai ba, amma ya bayyana jawabin a matsayin na ƙarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram