Yan bindiga sunyi garkuwa Baturen Ƴan Sanda wato D.P.O mai kula da karamar hukumar Nasarawa Eggon ta jahar Nasarawa, CSP Haruna Abdulmalik.
Anyi garkuwa da jami’in dan sandan ne a yayi da suke wani sintiri akan titin Nasarawa Eggon zuwa Akwanga.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa rahotanni na cewa, Yan bindigar sun tuntubi iyalan jami’in dan sanda inda suka bukaci da a basu naira miliyan ashirin a matsayin kudin fansa
Hakazalika Jaridar ta ce tayi kokarin zantawa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar yan sandan jahar A.S.P Ramhan Nansel amma hakan bai yiwuwa ba, har zuwa lokacin hada rahoton.
Sai dai mataimakin Shugaban Ƙaramar hukumar Benjamin Kuze ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.