Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna
Wata kungiyar matasa dake fafutukar ganin dan takarar jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya zamo shugaban kasa a zabukan 2023 mai suna Atiku ne Mafita a Najeriya dake kudancin jihar Kaduna ta ce bisa la’akari da halin da kasar ta tsinci kanta a ciki tun bayan hawan gwamnatin APC da ya shafi tabarbarewar tsaro da tsadar rayuwa da rarrabuwar kan ‘yan kasa babu wata mafita face zabar dan takarar da ya san kan tattalin arziki, Alhaji Atiku Abubakar.
Shugaban kungiyar na Kudancin Kaduna, Mujaheed Muhammad ne ya bayyana haka a bayan kammala taron kungiyar reshen karamar hukumar Jama’a a garin Kafanchan.
Mujaheed, yace bai kamata ‘yan Najeriya su sake ruduwa da duk wani alqawarin da jam’iyyar APC zata sake yi musu ba domin, “duk abubuwan da su kayi mana alkawari a 2019 ne fa suke sake maimaitawa suke kamfen da su wanda hakan ke nufin su da kansu sun tabbatar da cikin shekaru takwas ba su iya ceto Najeriya daga duk irin matsalolin da suka ce tana damunta ba.” Inji shi.
Yace lokaci yayi da ‘yan Najeriya zasu gwada Atiku Abubakar domin a cewarsa shine wanda zai iya dawo da martabar Najeriya saboda kwarewarsa a fannoni daban-daban da kuma irin karbuwar da yake da shi a kowane sassa na Najeriya ba wai kokarin kakabawa mutane wani mutum daban ba.
“Lokaci yayi da wasu tsiraru zasu daina firgita ‘yan Najeriya kan zabar Atiku domin shi kadai ne a cikin ‘yan takarar da kowace jam’iyya ta tsayar wanda mabiya kowane addini daga dukkanin sassan Najeriya suka aminta da shi kuma yake martaba dokokin kasa dana hukumar zabe ba tare da bayar da ciwon kai ba.