Mazauna Kano Sun Koka Kan Rushe Azuzuwa Domin Gina Shaguna

Mazauna garin Kano sun nuna takaicin su na cigaba da cin iyakar Makarantar Sakandaren Kofar Nassarawa da akafi sani da GSS K)Nasarawa, inda aka ga an rushe Azuzuwa domin baiwa ƴan kasuwa damar gina Shaguna.

Mazauna yankin da Ƙungiyoyin Fararen Hula a garin suka fara nuna damuwar su kan yawan bada filaye na Asibitoci, da Masallatai, da Filayen Ƙwallo, da wasu domin gina wuraren kasuwanci.

Rahotonni sun nuna cewa an fara katangar kuma tuni an bada azuzuwa domin gina Wurin kasuwanci, wanda take kusa da Filin wasan ƙwallo na Sani Abacha, tuni an Saida su ga wasu domin gina shaguna.

Bayan katangar makaranta data wuce ta kan hanyar IBB kusa da kasuwar Kwari an saida wurin.

A lokacin da Daily Trust ta ziyarci wurin a jiya, ta gano ginin shagon tuni an kafa shi, kuma Babbar Mota ta rushe wasu Tsaffin Azuzuwa.

Wani Ɗan Kasuwa kusa da wurin ya shaida cewa an rushe wasu Azuzuwa dake bayan katangar Makarantar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram