Mutanen Katsina Nura Khalil Ya Yarda Da Ku Ku Ma Ku Yarda Da Shi – In ji Adam Rabe Kafinta

*KADAN DAGA CIKIN TSARIN ENG NURA KHALIL IDAN KUKA ZABESHI YA KAFA GWAMNATI.*

Daga Adam Rabe kafinta

kowa yasan cewa a jihar katsina muna cikin yanayi da kalu bale dake nuna cewa gwamnati mai ci a yanzu ta gaza, gwamnati batada tsari mai kyau na samar da ci gaba dakuma ababen more rayuwar al’ummar jihar katsina. Idan muka zabi Eng Nura khali zaya inganta rayuwarmu da walwalarmu da jin dadinmu da kuma inganta karatun yayanmu da yayyenmu da kuma qannenmu.

Sanin kowa ne cewa Eng Nura khalil tsayayyen mutum ne kamili mai nagarta kuma mai son ci gaban jihar katsina da kewayenta, mutum ne mai kishin talakkawa kuma wanda kullum gurinshi shine ya za’ayi a kawo wani tsarin bai daya wanda zaya inganta rayuwar al’ummar jihar katsina baki daya. idan muka dubi ayyukan alherinsa da kuma ayyukan jinkai da gidauniyarsa take gudanarwa babu dare babu rana a fadin jihar katsinarmu baki daya.

Zanyi magana akan wasu muhimman abubuwan da Eng Nura khalil ya dade yanayi a fadin jihar katsina.

Gidauniyar Eng Nura khalil gidauniya ce mai zaman kanta wadda duk kudaden da take kashewa daga aljihunshi suke fitowa halaliyarshi ce, guminshi ne, zufarshi ne. Bai taba rike wani mukamin gwamnati ba bare ayi zargin cewa kudaden al’umma ne.

Anyi hasashen cewa Nura khalil yanama gidauniyarsa kasafin kudin da yakai naira million 50 zuwa million 70 a kowace shekara tundaga shekarar 2010 har zuwa wannan shekarar da muke ciki ta 2022, babu fashi babu alamun gajiyawa duk shekara ana fiddama gudauniyarsa wadannan makudan kudaden domin ragema talakkawan jihar katsina radadin zalunci da almundahanar da gwamnatocin jihar sukeyi da kudadensu.

Kadan daga cikin Ayyukan sune kamar haka:-

1- Biyama dalibai kudin jarabawa a matakin secondry school wanda gwamnatin jihar katsina mai ci a yanzu ta dakatar da biyama kowa sai yan tsiraru.

2- Daukar nauyin koyar da matasa maza da mata sana’a kala-kala da kuma basu tallafi mai tsoka wanda zasuyi jari.

3- Ziyartar gidan kaso domin fitar da wadanda aka daure sabida bashi ta hanyar biua masu wannan bashin da ake binsu.

4- Bada tallafin magunguna da kayan haihuwa ga asibitoci kyauta.

5- Daukar nauyin karatun marayu tundaga matakin primary school har zuwa jami’a wanda sabida wannan kokarin har mai dakinsa wato Hajiya Farida Muhammad Barau ta samu lambar yabo watau “GMK” Garkuwar marayun katsina.

6- Raba forms da kuma scratch cards na jamb kyauta ga daliban jihar katsina a kowace shekara

7- Ciyar da almajirai abinci kowace rana a jihar katsina da kewaye.

8- Samar da generators ga masallatai da makarantun islamiyyu kyauta shima duka a cikin jihar katsina.

9- Gyara rijiyoyin burtsatse wadanda gwamnati tayi kuma ta barsu a lalace domin amfanin al’ummar jihar katsina.

10- A satin da ya gabata ne kuma Eng Nura khalil ya Ware naira million hamsin ₦50’000’000 lakadan ba ajalan ba domin tallafawa yan gudun hijira dan rage masu radadin ibtila’in da ya fada masu na rabasu da dukiyoyinsu da kuma rayukan yan uwansu sanadiyyar sakacin gwamnatinmu.

Wannan shine kadan daga cikin ayyukan da Eng Nura khalil yakeyi dan ci gaban al’ummarmu kuma yanayinsu ne da halaliyarsa duba da cewa shi ma’aikaci ne mai zaman kansa wanda bai taba rike wani mukamin siyasa ba a gwamnatancen.

Ina tunatar da al’ummar jihar katsina cewa Gwamnati ta gaza amma Eng Nura khalil bai gazaba kuma bazaya taba gazawa ba wurin hakilon ganin al’ummarmu sun sami nagartacciyar rayuwa.

A karshe Ina jan hankalin al’ummarmu na jihar katsina da mu fito kwanmu da kwal-kwata mu goyama Eng Nura khalil baya a zaben nan na 2023 dake tafe domin inganta rayuwarmu da rayuwar yayanmu kamar yanda shima ya goya mamu baya a lokacin da ake zaluntarmu.

Nura Khalil ya yadda daku, kuma ku yadda dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram