Wani bincike daga masana a bangaren hada haɗar man fetur ya bayyana cewa a kasa da wata guda yan Najeriya sun sha litar mai sama da Biliyan biyu a tsakanin su.
Yayin da yawan kuɗin man da suka sha ya tammasam Naira Biliyan 340, Amar yadda rahoton nasu ya bayyana.
Yanzu haka dai a satin nan matsalar karancin man fetur ya karu a wasu sassan kasar nan, musamman Legas, da Abuja, wanda hakan ya sanya ƙaruwar farashin Ababan hawa ga al’umma.
Hakan na faruwa ne daidai lokacin da wasu masu kasuwancin man ke zargin tsadar man Dizal, da zama kan makarbiya wajen wahalar man fetur din.
Yayin da wasu kuma ke zargin kamfanin man ma kasa NNPC da rage yawan man da ake basu daga miliyan 103, zuwa miliyan 65, bayan zargin da wasu jami’an gwamnati suka yi cewa ana shigo da man ba bisa ka’ida ba tare da cin kasuwar sa.
Kawo wannan lokaci wasu daga cikin gidajen mai na ci gaba da siyar da duk lita ɗaya kan kudi Naira 165, amma suna fama da matsalar Dogayen layuka.
Wasu kuma kan Siyar sa shi daga 200 zuwa sama, kuma ba a fiye samun layi ba a wadannan gidajen mai.
A nasa bangaren shugaban kasa Muhammad Buhari yayin zanyawa da wata jaridar Amurka, ya ce bashi da wata niyya ta biyewa bankin Lamuni na duniya da sauran su cewa ya janye tallafin man fetur din.