Neman Mafaka: Yan Ci-rani 18 Sun Mutu A Yankin Melilla Na Ƙasar Sifaniya

Neman Mafaka: Yan Ci-rani 18 Sun Mutu A Yankin Melilla Na Ƙasar Sifaniya

‘Yan ci-rani 18 ne suka mutu wasu kuma suka samu raunuka a lokacin da gungun jama’ar suka yi kokarin tsallakawa zuwa yankin Melilla da ke arewacin Afirka zuwa kasar Sifaniya, kamar yadda jami’ai daga makwabciyar kasar Maroko suka bayyana.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin wadanda suka mutu sun fado daga saman shingen kan iyaka ne.

An kwantar da jami’an tsaro da bakin haure da dama a asibiti domin kula da su sakamakon arangamar da aka yi a safiyar ranar Juma’a.

Wannan dai shi ne karon farko da aka yi yunkurin tsallaka wa jama’a tun bayan da kasashen Sifaniya da Maroko suka dawo da huldar diflomasiyya a watan Maris.

Tabarbarewar dangantakar ta zo ne bayan da Sifaniya ta goyi bayan shirin cin gashin kai na Maroko ga yankin yammacin Sahara da ake takaddama a kai.

Jami’an kasar Sifaniya sun ce mutane dari da dama ne suka yi kokarin kutsawa cikin yankin bayan hana su shiga kasar.

An tilastawa yawancinsu koma baya amma sama da 100 ne suka samu shiga, kuma ana sarrafa su ne zuwa wata cibiyar karbar baki, in ji su.

Melilla da Ceuta, wani yanki na Sifaniya, a cikin ‘yan shekarun nan ya zama wurin da akasarin bakin haure na kudu da hamadar sahara ke yunkurin isa Turai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram