Tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa da ta kunshi runduna ta 302 ta sojojin Najeriya, jami’an sojin ruwa, DSS da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya sun tarwatsa sansanonin IPOB da kuma ESN a Idara, da kauyukan Nnebo, Ihe Mbosi da Ukpor dake karamar hukumar Nnewi ta kudu a jihar Anambra.
Sanarwar da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce, “A wani samame da sojojin suka kai da sanyin safiyar ranar Asabar 25 ga watan Yunin 2022, sojojin sun fatattaki ‘yan kungiyar ta IPOB wanda suka bude musu wuta tare da tarwatsa na’urorin fashewa domin fatattakar ‘yan ta’addan daga maboyarsu.
“A yayin samamen, sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, mujallu uku dauke da harsashi biyar na mili mita 7.62mm (na musamman) da alburusai guda biyar, bindigogin fanfo guda biyu da kuma bindigar gida guda daya.
“Sauran kayayyakin sun hada da injinan samar da wutar lantarki guda uku, da sauransu.
“Kazalika, sojojin bataliya ta 103 sun kai wani samame a sansanin IPOB da ESN dake dajin Nkwere Inyi a karamar hukumar Oji ta jihar Enugu.
“Haɗin gwiwar rundunar jami’an tsaron ya tilasta wa masu laifin tserewa cikin ruɗani, yayin da sojoji suka kwato motar Lexus da Toyota Highlander SUV da ake zargin miyagu sun yi awon gaba da su.
“Sauran kayayyakin da aka gano sun hada da babura biyu, bindigar ganga biyu da kuma harsashi guda bakwai masu rai.
“An umurci jama’a da su ci gaba da tallafa wa sojoji da sahihan bayanai kan ayyukan masu aikata laifuka a yankin.”