Kungiyar KDF Da Ke Goyon Bayan Mustapha Inuwa Ta Ce Ta Koma Ga Dikko Radda

Kungiyar Katsina Democratic Forum KDF ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar gwamnan jihar katsina a karkashin jam’iyyar APC, Dikko Umar Radda.

Shugaban kungiyar Gambo Dan Agaji ne ya bayyana haka a yayin da kungiyar ta kirawo taron manema labarai a yau Lahadi a Ofishin yakin neman zaben dan takarar gwamnan da ke Katsina.

Dan Agaji ya ce su da Kansu suka yanke hukuncin su yi mubayi’a ga tafiyar Dikko Radda tunda dai dama tun farkon tafiyar su ke addu’a da neman Allah ya zaba ma Katsina wanda ya fi zama alheri kuma Dikko Radda Allah ya zaba don haka sai a bi zabin Allah kawai.

Shugaban ya kuma ce su tun da su ke tafiyar Mustapha Inuwa babu wanda ya taba basu ko sisi ya kara da yi ma mambobin kungiyar cewa wannan tafiyar za su rinka samun ko da kudin mota ne na zuwa da komawa.

 

A nashi jawabin dan takarar gwamnan Dikko Radda, wanda Kabir amoga ya wakilta ya bayyana farincikinshi game da goyon bayan na su tare da tabbatar ma su cewa in har Allah yasa ya zama gwamna zai yi iya kokarin shi don ganin ya fidda al’umma daga cikin kuncin rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram