Mutane 17 Sun Jikkata Sakamakon Mamakon Ruwan Sama A Yobe

 

Mutane 17 ne suka samu raunuka daban-daban sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Dr. Mohammed Goje, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe, (SEMA), ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Damaturu ranar Lahadi.

Ya ce lamarin, wanda ya faru da karfe 12:30 na daren Lahadi, ya kuma haifar da ambaliya a cikin al’ummomin da ke cikin babban birnin, wanda ya kai ga rushewar gini.

Daga cikin wadanda suka jikkata a cewarsa, akwai mutane 6, yara 7, da kuma jarirai 4.

“Da misalin karfe 12:30 na daren Lahadi bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a Damaturu, wanda ya yi sanadin ambaliya a cikin al’ummomin da ke bayan White House da kuma yankin Ali Marami, Yobe SEMA ta samu kiran rugujewar gini tare da yara da jarirai da ke makale a ginin.

“Tare da tallafin masu sa kai, SEMA ta sami damar kwashe dukkan mutanen 17 da abin ya shafa daga gidaje 4 da abin ya shafa.

“A halin yanzu wadanda abin ya shafa suna kwance kuma suna karbar magani kyauta a asibitin kwararru na jihar Yobe, dake garin Damaturu,” in ji shi.

Ya yaba wa tawagar likitocin da ke sashin hadurruka da ayyukan gaggawa na asibitin kwararru na jihar bisa namijin kokarin da suka yi wajen kai dauki ga wadanda abin ya shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram