SERAP Ta kai Karar Buhari Kan Batan Kudin Wutar Lantarki Na Naira Tiriliyan 11

Kungiyar (SERAP)’ ta shigar da kara a kan shugaban kasa Muhammadu Buhari “a kan gazawarsa wajen gudanar da bincike a kan zargin cewa sama da Naira Tiriliyan 11 da aka samar don samar da wutar lantarki na yau da kullun tun daga 1999 na iya yiwuwa an sace su, ko kuma an karkatar da su zuwa aljihun gwamnati. ”

A kara mai lamba FHC/L/CS/1119/2022 da aka shigar a makon jiya a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman “umarni da doka ta tilastawa shugaba Buhari ya binciki yadda sama da Naira Tiriliyan 11 samar don samar da wutar lantarki na yau da kullum. ana zargin gwamnatoci sun wawashe tun a 1999.”

An ba da rahoton cewa wutar lantarki ta ruguje a kalla sau uku a cikin watanni biyar, da kuma sau 130 a cikin shekaru 7, lamarin da ya jefa gidaje da dama a fadin kasar nan cikin duhu.

A cewar Bankin Duniya, samar da wutar lantarki wacce zata kawo ta dauke yana sa ‘yan kasuwa Najeriya yin asarar kusan dala biliyan 29 a duk shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram