Wallahi Mun Yi Nadamar Zabar APC Sabuwar Jam’iyyar NNPP Ita Ce Mafita Ga Talaka – Abubakar Sadiq Usman

Matsalar Tsaro Yanzu har Cikin Kwaryar Garin Katsina ake Satar Mutanen kamar Rahamawa Sokoto rima da bayan Kttv

daga Abubakar Sadiq Usman

Munyi Allah wadai da wannan sakacin Gwabnatin APC Munsani cewa a duk lokacin da muka zabi gwamnati Sai sunyi rantsuwar kare lafiyar Al’ummar ta da dukiyoyinsu Amma Kash!!! wannan gwamnati taci Amana ta kasa Kare dukiyoyin Al’ummarta bare rayukansu, sun bari Yan ta’adda sunacin Karen su babu babbaka kullun mutane suna barci da zullumi,fargaba da tsoro.

Hakika wannan Yana daya daga Cikin abinda muka gani Yana faruwa shekara kusan 12 a mulkin PDP har muka sauya sheka Kuma nadawo APC tunanin mu APC zatafi kula da Al’ummar ta tare da basu kariya sai karshe muka Gane cewa gaba daya duk kanwar ja!! ce da PDP Da APC din….Wallahi munyi nadamar zabar APC kuma insha Allahu Rabbi Sabuwar Jam,iyyar NNPP itace mafitar talaka saboda Wanda suka kirkireta da wadanda ke cikinta ba mutane bane Wanda son duniya yake gabansu ba ko dukiyar talakawa

A karshe muna jajantama Wanda iftila’in ya fada dasu a mamadin Mai gidan mu Engr Nura Khalil da uwar gidansa Hajiya farida barau ..muna rokon Allah da ya bamu kariya ya kawo Mana karshen zubar da jinin da ake ba gaira babu dalili.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram