Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwanso, ya ce jam’iyyar APC da PDP sun gaza a tsawon shekaru wajen samar da tallafi ga tattalin arzikin jama’a da cigaba ga ‘yan Najeriya a dukkan bangarorin mulki.
Tsohon gwamnan jihar Kano wanda ya bayyana hakan a karshen mako a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti yayin wata ziyarar tuntuba da ya kai jihar ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da jam’iyyun biyu a babban zaben shekara mai zuwa, yana mai cewa dukkan alamu na ci gaban zamantakewa da tattalin arziki kullum suna tashi a cikin mummunan gefe.
Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda hanyar Akure zuwa Ado ke tabarbarewa, inda ya yi Allah-wadai da yadda gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi karkashin jam’iyyar APC suka yi watsi da jama’a suna shan wahala a kan hanya.
Kwankwaso ya bukaci jama’a da su ci gaba da rike amana tare da NNPP domin kawo sauyi ga kasar nan da dora ta kan turbar ci gaba.
Ya bayyana cewa jam’iyyar na fuskantar karuwar mambobi a cikin ‘yan watannin da suka gabata tun bayan da ya shiga dandalin.
Kwankwanso ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ake ta fama da ita a fadin kasar nan da kuma munanan manufofin tattalin arziki wadanda suka haifar da fatara, rashin aikin yi, hauhawar farashin kayayyaki sun isa ya sa jama’a su yi watsi da jam’iyya mai mulki, ya kara da cewa, “Hanyar da muke tafiya a yanzu ita ce hanya guda ta bala’i. a kasar.”