Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a yau 28 ga watan Yuni wanda zai kai ziyarar aiki kasar Portugal bisa gayyatar da shugaba Marcelo Rebelo de Sousa ya yi masa.
Shugaban kasar zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed; Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo; Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Pantami.
Sauran sun hada da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj-Gen Babagana Monguno (rtd); Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar da shugaban hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) Honorabul Abike Dabiri-Erewa.
Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaba Buhari wanda zai tattauna da takwaransa na kasar Portugal, za a karrama shi da lambar yabo ta kasar tare da yi masa ado da ‘Great Collar of the Order of Prince Henry’.
Ya ce ana sa ran shugabannin kasashen biyu za su jagoranci wani gagarumin taron kasashen biyu, da kuma shaida rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin da batutuwan da suka shafi kasashen biyu.
Shehu ya kara da cewa shugaba Buhari zai kuma ziyarci majalisar dokokin kasar Portugal inda zai tattauna da shugabanta Dr Augusto Santo Silva da kuma firaministan kasar Portugal Antonio Costa.
Ya ce a yayin ziyarar, shugaban kasar zai yi jawabi a wani taron ‘yan kasuwan Najeriya da na Portugal da kuma ganawa daban-daban da zababbun manyan jami’an gudanarwa na kasar Portugal da masu son zuba jari a Najeriya.
Buhari, a cewar sanarwar, zai kuma halarci taron Majalisar Dinkin Duniya kan teku, wanda aka fara a Lisbon a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni, wanda zai gudana har zuwa ranar 1 ga watan Yuli.
Sanarwar ta ce taron, wanda gwamnatocin kasashen Kenya da Portugal suka dauki nauyin shiryawa tare da goyon bayan Sashen Tattalin Arziki da Zamantakewa na Majalisar Dinkin Duniya (DESA), na da nufin kara daukar sabbin hanyoyin magance matsalolin da ke fuskantar tekun duniya da yanayin muhalli.
Garba Shehu ya ce shugaban kasar zai tattauna da al’ummar Najeriya mazauna kasar Portugal kan al’amuran da suka shafe su da kuma abubuwan da ke faruwa a gida, inda ya ce zai koma Abuja ranar Asabar 2 ga watan Yuli.