Cutar Lassa Fever Ta Hallaka Mutane 158 A Jahohi 24 Cikin Watanni 6

Cutar Lassa Fever ta Hallaka rayukan mutane 158 a Jahohi 24 a wannan shekarar, kamar yadda Cibiyar dake kula da Manyan Cututtuka ta Ƙasa ta bayyana.

Hukumar NCDC a cikin rahoton data fitar a jiya, tace an samu ɓullar wannan cutar a cikin Ƙananan Hukumomi 99.

Tace dukkanin su an tabbatar da cutar, kashi 68 daga Ondo suke (kashi 29), Edo nada Kashi 25 a yayinda Bauchi keda kashi 14.

“Mutanen da lamarin yafi shafa sun kasance masu shekaru 21 zuwa 30 (daga Shekara 1 zuwa shekara 90. Yanayin mata da maza da suka kamu ya kunshi 1:0.9,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

“Waɗanda cutar ta kama daga sati ka farko zuwa 24 na Shekarar 2022, yakai mutuwar mutane 158 ya rage daga kashi 19.8 idan aka kwatanta shi da Shekarar 2021.

Hukumar NCDC tace adadin sabbin mutanen da aka kama ya karu da 7 a cikin sati zuwa 23. An samu wannan ne a Jahohin Ondo, Edo, da Filato.

Tace an samu ƙaruwa idan aka kwatanta shi da na Shekarar 2021.

Babu wani Ma’aikacin lafiya da cutar ta shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram