Dalilin Da Yasa Naba Alumma Umarnin Riƙe Makamai – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa umurnin da ya bayar na yin kira ga mutane da su mallaki makami shi ne su kara kaimi ga kokarin jami’an tsaro a yakin da ake yi da ‘yan tada kayar baya.

Ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin yayin da yake kaddamar da kwamitoci na musamman guda hudu a gidan gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa an kaddamar da kwamitocin ne domin tabbatar da aiwatar da matakan tsaro da ake dauka domin magance matsalar ‘yan fashi da makami a jihar.

Kwamitoci na musamman guda hudu da aka kafa a yau sun hada da Kwamitin tattara bayanan sirri da masu ba da labari na ‘yan fashi, Kwamitin hukunta laifukan da suka shafi ‘yan fashi, Gudanar da Jami’an Kare al’umma da Kwamitin Tsaro na Musamman.

Matawalle ya bayyana cewa, a ‘yan makonnin da suka gabata, Zamfara ta fuskanci hare-haren ‘yan ta’adda a al’ummomi daban-daban, musamman a kananan hukumomin Bukkuyum, Gusau da Gummi na jihar.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da lalubo dabarun murkushe kalubalen tsaro da irin wahalhalun da ‘yan kasar ke fuskanta a hannun ‘yan ta’adda.

Ya yi nuni da cewa gwamnati na sane da kokarin jami’an tsaro wajen magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita, sai dai gwamnan ya bayyana cewa kokarin da sojojin ke yi ya samu cikas saboda rashin kayan yaki na zamani da isassun ma’aikata, don haka ne ya yanke shawarar cewa. jama’a su samo makamai don kare kansu daga ‘yan ta’adda.

Gwamna Matawalle ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samar da motocin Hilux guda 20 da babura 500 ga kwamitoci na musamman domin saukaka musu ayyukansu da zirga-zirga.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram