Kotu Ta Ɗage Shari’ar Nnamdi Kanu Zuwa 14 Ga Watan Nuwamba

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage shari’ar shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu kan zargin ta’addanci har zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.

Sai dai Kanu zai ci gaba da kasancewa a hannun hukumar tsaro ta, DSS, har zuwa ranar da aka sauya sheka daga shari’ar.

Mai shari’a Binta Nyako ta dage shari’ar ne biyo bayan daukaka karar da babbar kotun ta shigar na tabbatar da tuhume-tuhume bakwai da ake zargin Kanu dashi.

Mai shari’a Nyako dai ta yi watsi da tuhume-tuhume 8 cikin 15 da gwamnatin tarayya ta ke yiwa Kanu tare da bayar da umarnin gurfanar da shi kan sauran tuhume-tuhume 7.

Sai dai a zaman na ranar Talata, lauyan Kanu, Mike Ozekhome SAN, ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa ya shigar da kara a kotun daukaka kara da ke Abuja yana kalubalantar laifuka bakwai.

A karar da aka shigar mai lamba CA/ABJ/CR/625/2022, Kanu, ta hannun Ozekhome SAN, ya roki kotun daukaka kara da ta soke tuhume-tuhume bakwai da ake yi masa.

Ya bayyana karar da ya shigar a kan cewa laifuffukan da ake tuhumar sun aikata a wajen gabar tekun Najeriya, don haka babu wata kotu a kasar da ke da hurumin yi masa shari’a.

Ozekhome ya roki kotun da ta dakatar da ci gaba da shari’ar tuhume-tuhumen har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan batutuwan da aka gabatar gabanta.

Sai dai lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe, ya yi namijin kokari wajen shawo kan kotun ta yi watsi da hujjar Ozekhome bisa hujjar cewa dokar da ke kula da manyan laifuka (ACJA) 2015 ta hana ci gaba da shari’ar laifuka a kasar nan.

A wani takaitaccen hukunci mai shari’a Nyako ta amince da hujjojin Ozekhome tare da dage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba domin jiran sakamakon hukuncin kotun daukaka kara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram