Wata Ƙungiya Tayi Gargaɗin Gudanar Da Zanga-zanga Kan Dogon Yajin Aikin ASUU

Wata Ƙungiyar Fararen Hula mai rajin Kare Martabar Ilmi ta yi gargaɗin tattara Ɗalibai domin gudanar da zanga-zanga ta kasa baki ɗaya, idan har yajin aikin Malaman Jami’o’i ya cigaba da wakana.

Ƙungiyar ta bayyana baƙin cikin ta na ida lalacewar ilmi a Ƙasar, tana mai bayyana cewa Matsalar tsaro dake damun Jahohi da dama ya samu ne a dalilin lalacewar ɓangaren.

Shugabar Ƙungiyar Vivian Bello wanda y’ta bayyana matsayar Ƙungiyar ga Manema labaru a Abuja a ranar Litinin.

Bello yayi nuni dacewar Ɗalibai a Jami’o’in Najeriya sun yi kwanaki 725 basa zuwa Makaranta a dalilin yajin aikin ASUU a lokutta mabambanta a mulkin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Tace “ilmi ba abu bane da za’a tsaya ana tattaunawa domin babu abinda ya fishi. Matsalar Tsaro da muke fama da’ita a halin yanzu ya faru ne saboda lalacewar ɓangaren ilmi.

“Munyi dubi akan yadda ilmin manyan Makarantu ya lalace a Nijeriya.

“Ƙididdiga ta nuna cewa ASUU tayi yajin aiki na kwanaki 725, tun farkon wannan Gwamnatin wanda ya faru ne saboda rashin inganta jindaɗin su, baiwa Jami’o’i gashin kan su, da rashin kuɗaɗen tafiyar dasu.

“Idan aka duba an yi asarar shekaru biyu da rabi, a ilmin Ƴan Najeriya dake Makarantun Gwamnati a Ƙasar.

“Bashi ke ƙarshe ba. Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya da Fasaha da na Kwalejojin Ilmi suma suna cikin yajin aiki akan abu guda ɗaya.

“To idan muka duba da kyau, Ɓangaren ilmi yana Son ya ida lalacewa a Ƙasar”,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram