Ƴan Bindiga Sun Sace Mace Mai Tsohon Ciki Wata 9 A Zamfara

Wasu Yan bindiga da ake zargi, sunyi garkuwa da matar Tsohon Shugaban kungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi na Jahar zamfara, Alhaji Sanusi Gusau.

Majiyar Jaridar Jakadiya, ta gano cewa, Ramatu Yunusa na dauke da ciki kimanin wata Tara.

An dauke ta gidan Mijinta dake Damba Gusau da sanyin safiyar ranar talata.

Da yake jawabi, Mijinta wadda aka sacen, Malam Sanusi, ya bayyana cewa, Yan bindigar sun shiga gidan nasa da misalin Karfe daya na safiyar talata suka dauki matar sa Mai juna biyu.

A cewar sa, “abun baƙin ciki ne cewa lokacin babu wanda zai kawo masu dauki, koda kuwa Jami’an tsaron dake yankin ne.

” Sun haura ta katangar gidan, suka ɓalle min kofa, amma kafin su shigo Ɗaki na nasamu damar boye inda baza su ganni ba, saboda nasan cewa dama ni suka shigo dauka .

” A lokacin da suka bincike gidan duka , basu gano ni ba, abinda ya rage masu kawai shine su tafi da matar tawa mai ɗauke da juna biyu.

Ramatu, a cewar maigidan nata , tana iya haihuwa a kowane lokaci , tun daga lokacin da sukayi garkuwa da ita .

Ya Kara da cewa, har yanzu yan bindigar basu tuntube shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram