Ƴan Najeriya Sama Da Miliyan 29 Na Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi – NDLEA

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce kimanin ‘yan Najeriya miliyan 29.4 ‘yan shekaru tsakanin 15 zuwa 64 ne ke amfani da sinadarai masu sa maye da sauran muggan kwayoyi.

Kwamandan Hukumar NDLEA ta kasa reshen Jihar Anambra, Florence Ezeonye, ​​ne ta bayyana hakan a yayin wani bikin tunawa da ranar yaki da shan miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi ta Majalisar Dinkin Duniya ta bana a Awka.

Ta zana hoto mai ban tsoro na lamarin lokacin da ta ce daya cikin kowane hudu masu shan kwayoyi mace ce.

Ta ce: “Gaskiya a kasa ta nuna cewa akwai bukatar al’ummarmu su kara himma wajen wayar da kan jama’a game da illar shan muggan kwayoyi ga lafiyar dan Adam.

“Binciken amfani da muggan kwayoyi da binciken lafiya na shekarar 2018 ya nuna cewa kashi 14.4% na yawan amfani da muggan kwayoyi a kasar ya ninka kusan sau uku a duniya ndaga 5.6%. Abin da ya fi tayar da hankali shi ne cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ya shafi kowane matakin shekaru, jinsi, matsayin zamantakewa da yankuna.

“Daga binciken, ‘yan Najeriya miliyan 14.3 masu shekaru 15 zuwa 64 suna amfani da abubuwan motsa jiki kamar barasa, maganin kafeyin, nicotine da heroine, yayin da miliyan 10.6 ke amfani da tabar wiwi. Har ila yau, wasu miliyan 4.6 suna san magunguna fiye da kuma mafani da sinadarin opioids kamar hodar iblis wato codeine, tramadol, methamphetamine da morphine, da sauransu.

“Yana da matukar damuwa sanin cewa amfani da miyagun ƙwayoyi ya zama ruwan dare a tsakanin masu shekaru 25 zuwa 39, yayin da shekarun masu fara amfani da tabar heroin ya kasance shekaru 22, yayin da shekarun cannabis sativa ya kasance ya fi yawa ga masu shekaru 19.

“Musamman wadannan kungiyoyin shekaru sun hada da matasa wadanda ko dai a makarantun sakandare ko manyan makarantu ko kuma ke gab da kammala karatunsu.

“Don a sauƙaƙa rahoton binciken, matasa ne mafiya yawan masu shan muggan kwayoyi a Najeriya”.

Ta danganta matsalar da munanan yanayi wanda ya jefa mutane da yawa cikin munanan dabi’u daban-daban da ke haifar da rikicin tsakanin Al-umma da na rashin lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram