An ga jinjirin watan Dhul Hijjah a kasar Saudiya inda Gobe Alhamis ya zama daya ga wata.
Hakan yanuna cewa, Za a gudanar da hawan Arfa kenan a ranar Juma’a 8 ga watan Yulin shekarar 2022, wanda kuma Ranar Sallah zai kama Asabar 9 ga watan Yuli.
Hukumomin kasar ne huka sanar da hakan a shafin suna facebook mai suna Harafaini Sharafaini.
Idan za’a iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, hukumomin saudiyya a jiya sun bada sanarwar fara duba jinjirin watan na Dhul Hijjah.
Sai dai a gefe guda har yanzu a Najeriya a na dakon sanarwar ganin watan na Dhul Hijjah da ga fadar mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar Na Uku