Ortom Ya Jaddada Cewa Dole Gwamnati Ta Saki Nnamdi Kanu

Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom ya yi kira ga gwamnatin taraiya da ta saki jagoran ƙungiyar BIAFRA, Nnamdi Kanu.

Ortom ya yi wannan kira ne a wata hira da ya yi ta kai-tsaye a tashar telebijin ta Arise News a yau Laraba.

A cewar Ortom, ba wani laifi Kanu ya aikata ba sabo da shi yana rajin samar wa al’umma ƴanci ne, amma gwamnati ta kama shi kuma tana ci gaba da tsare shi.

Ortom ya ƙara da cewa irin ta’asar da Fulani masu fashin daji ke yi ya fi laifin da a ke tuhumar Kanu da shi amma an ƙyale su su na cin karensu ba babbaka.

“Ni kai na mutane nawa Fulani su ka kashe min a jiha ta amma ba a yi komai ba, sai dai a kama Kanu, wanda shi ɗan gwagwarmayar neman ƴancin talakawa ne, ayi ta tsare shi.

“Ina kira ga gwamnatin taraiya da ta saki Kanu domin ba laifi ya aikata ba,” in ji Ortom.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa jam’iyar PDP ba ta kyauta ba wajen hana Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike takarar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa.

A cewar Ortom, Wike shi ne ginshikin PDP tun da ga lokacin da ta faɗi a zaɓen 2015, inda ya ƙara da cewa hana shi takara da aka yi to an yi masa butulci kuma.ba a kyauta masa ba.

Gwamnatin Taraiya ta maka Kanu a kotu bisa zargin laifuka da suka dogara a kan cin amanar ƙasa da tada zaune tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram