Yanzu-Yanzu: Fayose Ya Watsar Da Tafiyar Atiku, Ya Fice Yace Dole Mulki Ya Koma Kudu

Tsohon Gwamnan Jahar Ekiti Ayodele Fayose ya buƙaci mulki ya koma yankin Kudu, yana mai cewa babu adalci Ɗan Arewa ya zama Shugaban Ƙasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala shekaru takwas.

Fayose, ɗan uwan Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike yana daga cikin waɗanda suka yi Takarar Tsayawa Shugaban Ƙasa a Babbar Jam’iyyar Hamayya, amma Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya lashe zaben.

Bayan zaben Fidda Gwani, Jam’iyyar PDP ta kira wani taron masu ruwa da tsaki domin tattaunawa akan yadda za’a kori Jam’iyyar APC daga mulkin Nijeriya.

Amma Jam’iyyar PDP ta fara fuskantar rikici bayan kammala zaben fidda Gwani, bayan Atiku ya zaɓi Gwamna Ifeanyi Okowa ta Jahar Delta a matsayin abokin takarar sa.

Atiku ya zaɓi Okowa akan Wike, duk da shawarwarin da wasu Shuwagabannin Jam’iyyar suka bada.

Jim kaɗan bayan haka, Goddsday Orubebe, tsohon Ƙaramin Ministan Harkokin Niger Delta ya fita daga Jam’iyyar.

A ranar Laraba, Fayose yace yanzu lokaci ne da yankin Kudu zasu fito da Shugaban Ƙasa.

“Tsarin Mulkin Jam’iyyar PDP ya bada damar a yi mulki na karɓa-karba. Sashe na 3 (c) yana cewa dole suyi amfani da wannan wajen zaben waɗanda zasu yi takara domin samun Adalci, gaskiya, da dai-dai to.

“Shugaban Ƙasa na yanzu yana kan wa’adin shi na biyu, wasu sunce dole ya zama yankin Kudu a 2023.

Awanni kaɗan kafin rubutun sa, Gwamna Samuel Ortom na Jahar Benue yace Wike ya kamata ya zama Abokin Takarar Atiku akan Okowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram