Ƴan Sanda Sun Hallaka Ƴan Bindiga A Jihar Anambra

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Anambra sun kashe wasu ‘yan bindiga biyu a Nkpor da ke karamar hukumar Idemili a jihar.

An ruwaito cewa, jami’an ‘yan sandan, yayin da suke sintiri a kan titin Obosi Nkpor, sun yi arba tare da kama ‘yan fashin a cikin wata farar mota kirar Toyota, da wata jar mota kirar Toyota Corolla da kuma babur.

 

Sai dai Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa, jami’an tsaron sun yi kacibus da ‘yan bindigar ne bayan fafatawa a tsakanin su, inda su Ka yi nasarar kashe biyu daga cikin su, tare da kwato wata bindiga mai sarrafa kanta, da karamar bindiga kirar guda, da dai sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram