Alhaji Atiku Abubakar Ya Magantu Kan Rikicin Jam’iyyar PDP.

Babbar Jam’iyyar Hamayya ta shiga rikici, bayan Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin abokin takarar sa a Shekarar 2023.

Matsaloli kan zaɓar Gwamnan Jahar Delta Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin Mataimakin Ɗan Takarar Shugaban ya na cigaba da ƙaruwa.

Wannan cigaba ya haddasa rashin amincewa mai ƙarfi a tsakanin Shuwagabannin Jam’iyyar, a yayinda wasu ke kira da’a cire Shugaban Jam’iyyar Dr. Iyorchia Ayu a matsayin Shugaban Jam’iyyar.

Dukkanin alamu sun nuna cewa Jam’iyyar ba’a dai-dai take ba, wanda ya sanya Gwamnoni biyu kaɗai ne suka halarci taron Ƙaddamar da Kwamitin neman yakin Gwamnan Osun a ranar Laraba, da Uwar Jam’iyyar tayi.

Da yake jawabi akan wannan lamari, Atiku yace suna bakin ƙoƙari domin su sasanta dukkanin rikice-rikice mn da Ƴaƴan Jam’iyyar ke fama dasu.

“Jam’iyyar PDP zata kasance da haɗin kan ta. Zata maida hankali akan aikace-aikacen ta. Muna bakin ƙoƙari domin magance matsalar. Haɗin kan mu shine abinda na baiwa fifiko. Matsayar mu ta hadin kan Nijeriya zai fara ne daga gida, zuwa Al’ummar mu.

“Kowane Gwamna, Ɗan Majalisa, da sauran Ƴan Majalisu da Jam’iyyu suka fitar ina girmama su. Idan suka yi magana ina sauraro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram