An Cafke Mutane 6 Da Zargin Kutsawa Gidan Ronaldo

An kama mutane 6 da laifin ɓalla gidan Euro miliyan 3 na gidan tsohon Ɗan Wasan ƙwallon ƙafan Brazil Ronaldo, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaru na AFP a ranar Alhamis ya tabbatar daga wata majiya.

Ɗan wasan Ƙwallon Ƙafa na Paris Saint-Germain, Marco Verrati na zaune a gida Ronaldo a Ibliza, Amma baya gida a lokacin da suka ɓalle gidan ranar Litinin tare da tafiya da gwala-gwalai da Kuɗaɗe.

An kama mutane 2 a tashar Denia a gabacin Spain, a yayinda aka kama guda 3 a kudancin garin Malaga, Inji wadannan Majiyoyi ga AFP.

A cewar Jaridar Spanish Press, huɗu daga cikin mutane 6 da aka kama sun kasance ƴan Albaniya, biyu ƴan Spaniya, sai wani ɗan Roma, Wanda ya sanya suka ƙware wajen ɓalle gidajen mutane.

Rahoton Jaridar Press ya bayyana cewa ƴan sanda sun gano da yawa daga cikin abubuwan da suka sace, wanda darajar takai Euro miliyan 3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram