Ɗiyan Ike Ekweremadu Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai ta Najeriya ya bayyana a kotun Uxbridge ta Majistare dake Landan, a lokacin da mahaifin su ya bayyana a Kotu a ranar Alhamis.
Ekweremadu da Beatrice matar, an kama su a satin daya gabata akan zargin Safarar yaro da yunƙurin cire masa wasu sassan jiki.
Duk da an ɗage Shari’ar zuwa 7 ga watan Juli na Shekarar 2022, amma tana sauri, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya bayyana.
Matar Ɗan Majalisar ta buƙaci Kotu ta bata dama taga mijin ta, saboda bata ganshi ba tun Alhamis data gabata, amma Kotu ta hana.
An tsare Ekweremadu in kurkuku, a yayinda Kotun tace kamar sa babban mutum, akwai ganganci ya sanya rayuwar sa a bautar da yaro.
Wannan cigaba ya zo ne awanni 24 bayan Shugaban Majalisar Dattijai ta sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta ɗauki ƙwararrun lauyoyi domin su taimaka mashi.
Lawan ya sanar da cewa an kafa wata tawaga domin ya hadu da Ekweremadu a Landan akan shari’ar.
Wannan lamarin na Ekweremadu ya fara bayan ya dauki yaro domin ya baiwa Ɗiyar sa koda.
A cewar Lauyoyi, tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar ya kawo yaron daga Nijeriya domin wannan lamari