Gwamna Fintiri Ya Ajiye Crowther Seth Ya Ɗauki Farfesa Farauta, A Matsayin Abokiyar Takara

Gwamna Fintiri Ya Ajiye Crowther Seth Ya Ɗauki Farfesa Farauta, A Matsayin Abokiyar Takara

Gwamnan Jihar Adamawa kuma ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 a jihar, Ahmadu Fintiri, ya ɗauki Farfesa Kaletapwa Farauta a matsayin abokiyar takararsa.

Mrs Farauta ita ce shugabar jami’ar jihar Adamawa ADSU, Mubi.

Mai magana da yawun gwamnan, Solomon Kumangar, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Alhamis a Yola.

Farauta dai ta fito daga Numan, a shiyyar kudancin jihar Adamawa.

A baya dai ta riƙe muƙamin shugabar hukumar kula da ilimin bai-ɗaya ta jihar Adamawa, ADSUBEB, sannan kuma ta riƙe kwamishinan ilimi.

Ta kasance malama a Jami’ar Modibbo Adama, MAU, Yola.

Farauta, wacce aka haifa a ranar 28 ga Nuwamba, 1965 a Numan, Kudancin Adamawa, tana da aure da ’ya’ya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram