Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Gwamnan Jahar Zamfara, Mohammed Matawalle ya goyi bayan kisa ga wanda aka kama da ta’addanci, garkuwa da mutane, Satar Shanu, da yan ƙungiyar asiri a faɗin jahar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne bayan ya sanya hannu akan Dokar Kudirin da majalisar dokoki ta jahar zamfara ta zartar, inda ta sanya hukunci mai tsauri akan Ƴan ta’adda, satar Shanu, Ƴan ƙungiyar mafiya, da masu garkuwa da mutane, da sauran manya manyan laifuffuka.
Matawalle ya bayyana cewa, a ƙarƙashin dokar, duk wanda aka kama da taimakon aikata ta’addanci, zaiyi zama gidan kaso na shekaru goma zuwa ashirin ba tare da bada zaɓin biyan Tara ba.
Ya jaddada cewa, gwamnatin sa a shirye take da ta yaki duk wani ɗan ta’adda a faɗin jahar a ƙarƙashin Doka, domin kare jahar da dawo da Zaman lafiya musamman ga al’ummar da Yayn ta’addan suka addaba.
“Sabuwar dokar ta bada damar hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da aikata laifin ta’addanci, garkuwa da mutane, satar shanu, ko kuma taimakon ƴan ta’adda da bayanan sirri, zai fuskanci hukuncin kisa
“A karkashin dokar, duk Wanda aka kama da laifin aikata ko bada gudunmuwa wurin aikata manyan laifuka , zaiyi Zaman gidan kaso na shekaru ashirin Ko shekaru goma, ba tare da bada damar biyan Tara ba.
“Babban abinda ko wace gwamnatin dake a fadin duniya ta Samar shine Zaman lafiya” kamar yadda ya bayyana.
Gwamna Matawalle, ya bayyana cewa kafa Jami’an tsaro na Al’umma baya da bambanci da Kungiyar Fararen hula da CJTF a jihar Borno da Amotekun a yankin Arewa maso Yamma.