Kotu Ta Dakatar Da Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Oyo

Wata babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan.

Mai shari’a Ladiran Akintola ya bayar da wannan umarni ne a ranar Larabar da ta gabata biyo bayan karar da mataimakin gwamnan ya shigar a gaban sa.

Ya kuma ba da umarnin a ci gaba da kasancewa har sai an yanke hukunci kan karar da mataimakin gwamnan ya shigar a kan ‘yan majalisar.

Daga nan ne kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 5 ga watan Yuli domin baiwa majalisar damar gabatar da amsarta kan ikirarin mataimakin gwamnan.

Olaniyan ya samu wakilcin lauyansa, Cif Afolabi Fashani (SAN) yayin da ‘yan majalisar suka samu wakilcin daraktan kula da harkokin shari’a, O Olabanji.

Bayan ficewar sa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC , majalisar da ke karkashin jam’iyyar PDP ta fara shirin tsige Olaniyan, inda 23 daga cikinsu suka sanya hannu kan takardar tsige shi.

Majalisar ta zargi mataimakin gwamnan da rashin da’a, da rashin biyayya da dai sauran zarge-zarge masu kama da juna.

Shi ma Olaniyan ya mayar da martani kan zargin da ake masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram