NDLEA Ta Cika Hannu Da Wata Dilar Ƙwaya A Jihar Rivers

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA tace jami’an ta sun kama wata mata Dilar Ƙwaya a Obunku ta Ƙaramar Hukumar Oyigbo ta Jahar Rivers.

Hukumar tace Matar mai suna Celina Ekeke, an kama ta da buhunna 24 na Tabar Wiwi da yawan ta yakai Kilogaram 231.2.

Sanarwar tace “a ranar Laraba, 29 ga watan yunin Shekarar 2022, Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Rivers ta gudanar da bincike a Obunku ta Ƙaramar Hukumar Oyigbo ta Jahar Rivers, Inda suka kama fitacciyar Dilar Ƙwaya da Buhunna 24 na girmanta yakai Kilogaram 231.2.

“Tuni dama ta kasance daga Jerin wanda Hukumar ta ke nema a yayinda take amfani da gurguwar kafar ta wajen saida miyagun kwayoyi.

“A halin yanzu tana kan bincike a Jihar Rivers.

“Kwamandan Jaha Kwamared Ahmed Mamuda, ta Jaddada gargaɗin dukkanin Dilolin Kwaya dasu guji saida ta, domin sai an tabbatar an kama ta, musamman yadda Shugaban Hukumar Birgediya-Janar Buba Marwa ya bada Umarni a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki akan Dilolin Kwaya.

“Zamu yi amfani da wannan damar muyi kira ga Al’umma dasu bamu bayanai masu inganci da zasu sanya mu wayar da Al’umma kan Miyagun Ƙwayoyi.

“Muna kira ga masu amfani da Ƙwaya dasu nemi taimako kafin lokaci ya ƙure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram