Birtaniya Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Nijeriya Kan Korar Baƙin-Haure

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa ta kulla yarjejeniya da takwararta ta Najeriya kan kamawa da mayar da bakin-haure gida.

A wani sako da ta sanya a tuwita Sakatariyar harkokin cikin gidan Birtaniya Priti Patel ta ce yarjejeniyar mai matukar muhimmanci da Najeriya za ta sa a samu damar kara fitar da miyagun masu laifi daga kasar.

Ta bayar da sanarwar ne a jiya Alhamis sa’o’i bayan Birtaniyar ta mayar da wasau ‘yan Najeriyar su 10 gida bisa laifukan da suka danganci shige da fice.

Ba a bar mmutanen sun gana da kowa ba ko ma ‘yan jarida a filin jirgin saman a Lagos inda aka dawo da su.

A farkon watan jiya, Yuni Kotun hakkin dan-Adam ta Turai ta haramta tashin jirgin farko da zai kai masu neman mafaka daga Birtaniya zuwa Rwanda.

Jirgin na daga shirin kai masu neman mafaka daga Birtaniya zuwa Rwanda, kamar yadda Birtaniyar ta sanar a watan Afrilu.

Shirin da gwamnatin Birtniyar ta ce zai hana masu bi ta tekun Ingila suna shiga kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram