Rasha Tayi Babban Kuskure Na Shiga Ukraine – Inji NATO

Sakatare-Janar na Ƙungiyar Ƙawancen Jami’an tsaro na Kasashen Turawa yace dagaske ne kuma a bayyane cewa Russia ta raina Ukraine Tayi tunanin ba tada ƙarfi.

A cewar sa, Shugaba Vladimir Putin na Kasar Rasha ya Kuma raina hadin kan Ƙawancen Jami’an tsaro na NATO , yana mai cewa yayi Babban Kuskure.

“Shi (Putin) yayi babban kuskure; gaba ɗaya ya raina ƙarfin da Jami’an tsaro na Ukraine ke dashi”, ya shaidawa gidan talabijin na CNN.

A cewar sa, Shugaba Putin har yanzu baiga ƙoƙarin da Shugaban Ƙasa Volodymyr Zelensky yayi da kuma Al’ummar Ƙasar Ukraniya.

Ya ce Shugaban Ƙasar Russia ya kasa cimma wasu daga cikin abubuwan da suka sanya ya shigar wa Ukraine da Faɗa, wanda yana nufin ya rage ƙarfin ƙawancen NATO.

Stoltenberg yayi amanna cewar kafin yanzu, Putin yana da ƙarfi sosai kuma yafi na NATO da mambobi guda biyu, Finland da Sweden, Wanda sun Kasance suna iyaka da Russia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram