Rundunar Sojin Ƙasa Ta Tabbatar Da Hallaka Dakarun Ta da Masu Yawa A Niger

Rundunar Sojin Ƙasa ta tabbatar da hallaka Dakarun ta a Karamar Hukumar Shirori ta Jahar Niger, inda suka kashe Jami’an tsaro da dama

Ciki har da Sojoji da Ƴan Sanda.

Sun kuma sace ƴan kasar China da dama.

Da yake tabbatar da harin, Rundunar Soji a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a nata ya fitar Birgediya-Janar Onyeama Nwachukwu yace a lokacin sun hallaka wasu ƴan Bindigar.

“Abun baƙin ciki, sojoji da dama sun hallaka a wurin musayar wuta a harin ta’addanci da aka kai masu.

” An gano wurin sannan an tura Dakarun Soji domin gano su, wanda tuni sun hallaka wasu ƴan Bindigar.

“Kwamanda na 1 na yankin tuni yaje wurin domin ɗaukar matakau”, inji sanarwar

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram