Ƴan Sanda Sun Kuɓutar Da Yara Kusan 50 Da Aka Ɓoyesu A Wata Cocin Ondo

Ƴan Sanda Sun Kuɓutar Da Yara Kusan 50 Da Aka Ɓoyesu A Wata Cocin Ondo

An gano yara da dama a wani gida da ke karkashin wani coci a garin Ondo na jihar Ondo.

Ana kyautata zaton an yi garkuwa da yaran ne a harabar cocin da ke unguwar Valentino a cikin Garin Ondo.

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Misis Funmilayo Odunlami, ta tabbatar wa gidan talabijin na Channels faruwar wannan lamarin

A cewarta, an kai yaran hedikwatar ‘yan sanda kuma ana ci gaba da bincike.

Majiyar jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa, An kama limamin cocin da wasu ’yan kungiyar kuma ana sa ran samun karin bayani daga wajan su kan lamarin.

Wadanda aka kama a halin yanzu ‘yan sanda na yi musu tambayoyi a sashin binciken manyan laifuka.

Ba a dai san adadin yaran da lamarin ya shafa ba amma ana kyautata zaton za su kai 50.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram