Babban jami’in tsaro wato dogarin marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya) ya ce biyayyarsa ga Najeriya ce ta sa ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Al-Mustapha wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance (AA) ya bayyana haka a lokacin da ya fito a matsayin bako a gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today.
“Na yanke shawarar a wannan karon na amsa kiran da yawa daga cikin dattawan Najeriya da matasa daga Arewa zuwa Kudu da kuma wasu makusanta da yawa da na yi aiki da su, na amsa kiran da aka yi min in tsaya takara.
“Sha’awar da muke da ita ga kasar nan ya fi ta yadda kalubalen da muke fuskanta jiya da kuma matukar godiya ga inda muke a yau, na wadanda suka damu da gaskiyata.
“Wannan sanin ya kamata, irin sadaukarwar da kuzarin kishin kasa ke yi ne ya sa mu ke fuskantar siyasa,” in ji Manjo Al-Mustapha.
Yayin da yake tabbatar da cewa ba ya cikin takarar shugaban kasa don neman kudi kamar yadda wasu ke zato, mai dauke da tutar kungiyar Action Alliance ya ce bayanai da dama sun nuna cewa Najeriya ta kasance wuri mara kyau a halin yanzu, don haka ana bukatar ‘yan Najeriya masu jajircewa wajen mayar da al’ummar kasar kan tafarki.
“Shekaru bakwai da suka wuce tun bayan da na fito daga gidan yari, muna gudanar da bincike a ciki da wajen Najeriya, kuma binciken da muka yi yana da matukar tayar da hankali.
“Abin da ya kamata kowane dan Najeriya mai kishin kasa ya yi a yanzu shi ne ya fahimci girman matsalolin da Najeriya ke fuskanta,” in ji dan takarar shugaban kasa na AA.
Ya kara da cewa “sabon tsarin duniya yana canzawa kuma ba mu canza ba, duniya tana gudana tare da lokaci kuma babu mu, mutane suna yawo da iska kuma ba mu; lokaci ya canza kuma mun kasance a tsaye.”
Da yake magana kan alakar sa da Janar Sani Abacha, Al-Mustapha ya ce ba ya nadamar aiki da marigayi shugaban mulkin soja.
“Ba ni da nadama, da zarar kun shiga aikin soja, ya kamata ku kasance da hankali don yin aiki a ko’ina.”
Majiyar Jaridar ta rawaito cewa, Manjo mai ritaya ya ce kaddararsa ce ta kai shi inda ya yi hidima kuma duk inda ya je ya yi aiki da himma, inda ya bar bayanan da ba za a iya gogewa ga tsarara ba.
Al-Mustapha, ya bayyana cewa ba zai so ya mayar da hankali ga aikin da Abacha kawai yake yi ba, sai dai ya duba yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa kasa hidima, da kuma yadda har yanzu yake sha’awar yin hidima ga kasar nan.