FRSC Ta Gargaɗi Direbobi Kan Tuƙin Ganganci A Cikin Damina

FRSC Ta Gargaɗi Direbobi Kan Tuƙin Ganganci A Cikin Damina

Hukumar Kula da Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa reshen Jahar Kano, ta gargadi Direbobi dasu yi tuƙi da kula domin gujewa hatsari musamman lokacin Damina.

Kwamandan Shiyya na Hukumar Zubairu Mato ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a Kano a ranar Asabar.

Yace dole Direba su siyo tayoyi masu kyau, sun duba dukkanin injin motar su, da ɓangaren haske, domin kiyaye lafiyar su.

“A lokacin da ruwa yayi ƙarfi, hanyoyi zaka same su da santsi.

“Motoci na buƙatar suyi tuƙi tsakanin kilomita 20 zuwa 30 akan babbar hanya, a yayinda ya kamata suyi tuƙi daga kilomita 10 zuwa 20 domin gujewa hatsari,” Inji shi.

Mato yayi kira dasu kula da ramukan hanya, da masu tsallake hanyar a lokacin da suke tuƙi.

Ya ƙara dacewa FRSC za taje Tashoshi tare da wa’azantar da Direbobi dasu guji mugun gudu, da munanan tuƙi akan manyan hanyoyi domin magance hatsari.

Kwamandan Shiyyar ya ƙara dacewa, Hukumar ba zata gajiya ba wajen rufe ramukan hanyoyi ba a Manyan hanyoyi a matsayin wani aikin ta na cigaban Al’umma, tare da taimakon Kamfanoni domin magance hatsari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram