Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari
Olori Kafayat, ɗaya daga cikin matan marigayi tsohon Alaafin na oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi, ta rasu.
Ta Rasu ne, bayan wata biyu da rasuwar Sarkin na Oyo.
Olori kafayat, itace mata ta hudu ga marigayi tsohon Alaafin oyo, ta Rasu ne a daren ranar Juma’a.
Mahaifiyace ga Prince Adebayo Adeyemi, Wanda shine Shugaban Hukumar Fansho na Ma’aikatan Ƙananan na Jahar Oyo.
Har zuwa hada wannan rahoton babu cikakken bayanai dangane da yadda ta rasu.
Oba Adeyemi ya rasu a ranar 22 ga watan afirilu na Shekarar 2022, a asibitin Koyarwa na Jami’ar Afe Babalola, dake Ado -Ekiti, Babban birnin jahar Ekiti.
Yayi mulki na tsawon shekaru 83, inda daganan ya rasu.
Har ya zuwa yanzu, babu wani daya gaji karagar mulkin Oba Adeyemi, a matsayin Sarki, bayan rasuwar sa.