Sai Nan Da Shekaru 30 Kafin PDP Ta Kwace Mulkin Najeriya Daga APC – Oyetola
Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola ya ce jam’iyyar APC za ta doke jam’iyyar PDP a ranar 16 ga watan Yuli.
Dukkan jam’iyyun biyu za su gwabza junan su nan da makonni biyu masu zuwa a zaben gwamnan jihar.
Oyetola ya bayyana hakanne yayin ziyarci Ila-Orangun a karamar hukumar Ila ranar Juma’a.
“Za a dauki PDP shekaru 30 kafin ta farfado daga doke ta da za ta yi saboda shan kaye”, in ji shi.
Oyetola ya ce shekaru takwas da ya yi yana mulki a matsayin gwamna “ya tabbata da Allah ya na tare da shi”.
Ya shawarci jam’iyyun adawa da su yi shiri don gudanar da mulki maimakon takara.
Gwamnan, ya yi kira ga masu zabe da kada su sayar da kuri’unsu.
“Za su yi tafiya da kuɗi, amma ayyukansu ba za su yi rinjaye ba.”
Dan takarar na jam’iyyar APC ya kuma bayyana abokan hamayyarsa a matsayin masu dama.