Shugaban Ƙungiyar Ohaneaze Ya Buƙaci Inyamurai Da Su Ɗauki Dangana Kan Zaɓukan Fidda Gwani
Shugaban Ƙungiyar Inyamurai ta Ohaneaze Ndigbo Ambasada Farfesa George Obiozor, ya magantu kan fito da sunayen Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa da Manyan Jam’iyyu na APC da PDP suka yi domin Babban Zaɓen Shekarar 2023.
Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa daga yankin Kudu maso Gabas sun rasa takarar su a manyan Jam’iyyu a zaben fidda gwani, da wasu basu samu koda ƙuri’a ɗaya bace duk da neman da yankin yayi na fito da Shugaban Ƙasa, akan Adalci, da dai-dai, idan akayi mulkin karɓa tsakanin yankin Arewa da yankin Kudu.
A yayin da Bola Tinubu Tsohon Gwamnan jihar Lagos daga yankin Kudu maso Yamma ya samu nasarar zama Ɗan Takarar Jam’iyyar APC, Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar daga yankin Arewa maso Gabas ya zama Ɗan Takarar PDP, zaɓukan da ake gani anyi amfani da Dala domin samun nasara.
Amma Obiozor ya yi shiru akan sakamakon waɗannan zaɓukan Fidda Gwani, ya magantu a ranar Asabar da safe a cikin wata sanarwa “Mi Najeriya take so daga Ngigbo?”
Tsohon wakilin Nijeriya a Kasar Amurka yace “ta tabbata cewa Shuwagabannin Nijeriya sun hana yankin Kudu maso Gabas damar fito da shugaban ƙasa a 2023.
“Da wannan ya nuna rashin adalcin Shuwagabannin Nijeriya akan Inyamurai, fiye da tunani.”
Obiozor wanda ke neman lafiya a Asibitin Dubai, ya bayyana cewar daga rashin adalcin ta, ta baiwa kasashe kunya ta hanyoyi hudu.
A lokacin da yake kira ga Ndigbo da kada su damu matuƙa amma su jira suga abinda tarihi zai nuna.
Obiozor ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daga Sakataren Ƙungiyar Ohaneaze Ndigbo Dr. Alex Ogbonnia, ya godema ƴan Najeriya da suka goyi bayan Inyamurai su fito da Shugaban Ƙasa a 2023,akan tarihin Nijeriya na karba karba daga yankin Arewa da Kudu.