Ƴan Najeriya Na Cigaba Da Nuna Damuwa Kan Yawan Tafiye-Tafiyen Buhari Zuwa Ƙasashen Waje
Ƴan Najeriya na cigaba da nuna damuwa kan yawan tafiye-tafiyen Shugaba Buhari zuwa Ƙasashen Waje, tare da zargin cewa tafiye-tafiyen baya kawo wani alfanu ga kasar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadi.
Shuwagabannin Kasashe suna zuwa tafiye-tafiye ne domin halartar Wasu tarurruka masu amfani, da ƙulla alaƙa ta Diflomasiyya, ko kuma wani yarjejeniyar kasuwanci.
Tun bayan zuwan sa, Shugaba Buhari ya kasance cikin zarge-zarge kan yawaitar tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare, da caccaka cewa babu wani alfanu da ƙasar ke girba.
Wasu suna caccakar Buhari daya fifita tafiye-tafiyen ƙasashe waje, fiye da abubuwan dake faruwa a cikin Ƙasa.
Yawan ziyarce-ziyarcen dai ya samu tasgaro sakamakon cutar Covid-19, wanda ta hana taro na tsawon shekaru biyu.
Amma daga cire dokar Covid-19, Shugaba Buhari ya koma kan tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare.
A farkon shekarar nan, ƙididdiga ta nuna cewa yayi tafiya zuwa kasashen goma.
Ta ƙarshe daya je itace ziyara zuwa Ƙasar Portugal a satin daya gabata a wajen Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa. Ya kuma Ziyarci Ƙasar Landan a ranar 1 ga watan Juli.