Yajin Aikin ASUU: Ƴan Sanda Sun Tsaurara Matakan Tsaro A Abuja, Yayin Zanga-Zangar NLC

Yajin Aikin ASUU: Ƴan Sanda Sun Tsaurara Matakan Tsaro A Abuja, Yayin Zanga-Zangar NLC

Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun tsaurara matakan tsaro a kusa da Unity Fountain da ke Abuja, inda ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar da ma’aikata a karkashin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC suka shirya a fadin kasar nan.

Ma’aikatan na jihohi 36 na tarayyar Najeriya, sun fara zanga-zangar ne a ranar Talata, inda suka gargadi gwamnatin tarayya da ta yi watsi da kiran da suka yi na bude jami’o’in Najeriya, ta hanyar biyan bukatun kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato (ASUU) da sauran kungiyoyi uku.

Manema labarai, wadanda suka isa Unity Fountain da misalin karfe 7:15 na safiyar Laraba, sun lura cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya na jimge a wurin taron da alama don dakile duk wani alamu na sabawa doka da oda.

Daya daga cikin jami’an da ya zanta da Jaridar Daily trust, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun ranar Talata wasu takwarorinsa suka je wurin taron domin tsara dabaru da kuma dakile duk wani harin da za a iya kai wa, inda ya ce ba wai kawai an tura su domin zanga-zangar ba ne.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jami’an ‘yan sandan na tare da takwarorinsu na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da na civil defence wato (NSCDC).

Idan ba a manta ba, a ranar Talata ne shugabannin kungiyar ta NLC ta kasa ta bayar da umarni ga kungiyoyin kwadago sama da 50 da su hada hannu da ‘ya’yan kungiyar domin shiga zanga-zangar a babban birnin kasar Tarayya Abuja da sauran jihohin kasar nan

Duk da hakan, Tattakin wadda shugaban NLC, Ayuba Wabba ke jagoranta, ta shiga rana ta biyu a yau laraba kamar yadfa kungiyar kwadagon ta shirya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram