Ƴan Sanda A Jihar Kogi Sun Damƙe Tsoho Mai Shekara 50 Da Ya Hallaka Ɗiyar Sa Kan Tsafi

Ƴan Sanda A Jihar Kogi Sun Damƙe Tsoho Mai Shekara 50 Da Ya Hallaka Ɗiyar Sa Kan Tsafi

Wani mahaifi mai shekaru fiye da hamsin, mai suna Dauda Ibrahim daga Idah a karamar hukumar Idah ta jihar Kogi an kama shi da laifin yin garkuwa da diyar sa Sherifah mai shekaru goma sha biyar tare da kashe ta domin tsafi.

Wanda ake zargin wanda aka ce ma’aikaci ne na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Idah a sashin ayyuka da kashe gobara, an yi zargin cewa sun haɗa baki da wasu mutane biyu Isah Adams da kuma Adah daya domin aikata wannan ɗanyen aikin.

Rahoton ya ce an yi garkuwa da marigayiya Sherifah ne a ranar 4 ga watan Agustan 2022, a gidansu da ke Okenya kan titin Itayi a karamar hukumar Igalamela/Odolu a jihar.

An gano gawar yarinyar a cikin wani kabari mara zurfi kwanaki kadan bayan ɓacewar ta, tare da yanke jiki da wasu muhimman gabobin.

Rundunar ƴan sandan jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an kama wanda ake zargin tare da wadanda suka taimaka masa a kan haka.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Williams Ayah, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce kwamishinan ‘yan sandan, CP Edward Egbuka ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka da ke Lokoja.

“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Edward Egbuka, ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kan zargin yin garkuwa da mutane, kashewa da bacewar sassan jikin wata budurwa mai suna Miss Sherrifah, ‘yar shekara goma sha biyar a garin Idah da mahaifinta ya yi. ,” inji shi.

Rundunar ‘yan sandan ta bakin PPRO ta ba da tabbacin cewa ‘yan sanda za su gudanar da cikakken bincike a kan lamarin don gano musabbabin yin garkuwa da marigayiyar tare da kamo masu laifin da suka aikata laifin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Share via
Copy link
Powered by Social Snap