Dara Taci Gida: Matsafa Sun Kashe Abokanan Tsafin Su 2 A Bayelsa

Daga Wakiliyar mu Amira Salisu

Wasu yan kungiyar shan jini sun kashe matasa 2 da ake zargi ƴan ƙungiyar abokan hamayyarsu ne, a garin Ogbogboro dake Ƙaramar Hukumar Yenagoa ta Jahar Bayelsa.

Wani Mazaunin yankin ya shaidawa Majiyar Jaridar Jakadiya cewa, kisan baya rasa nasaba da bambance bambancen tsakanin kungoyin guda biyu a yankin.

Ana kiran mamatan da aka tsinta a ranar talata da suka ƙunshi Fati mai shekaru 30 da kuma Famizibe Clarkson mai shekaru 25, An kashe su a cikin Gidajen su dake yankin.

Majiyar ta bayyana cewa yankin yana cikin hatsari dangane da yanda yan mafiyar ke gudanar harkokinsu da kuma kai hari ga mutane a lokutan da suka gabata, yan kungiyar sun sake haɗa kansu domin gudanar da aiyukansu.

Jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jahar SP Asinim Butswat ya tabbatar da kisan, ya kuma bayyana cewa Rundunar ta fara bincike dangane da lamarin.

Ya bayyana cewa,” waɗanda aka kashe daya ƙunshi Tuesday Fati mai shekaru 30 da kuma Famizibe yar shekaru 25 an kashe su a ranar 11 ga watan Ogustan 2022 acikin Gidajen su a yankin Ogbogboro dake Yenagoa da misalin ƙarfe 3:30 na dare

An kwashi gawarwaki zuwa dakin ajiye gawa dake asibitin Babbar Tarayya ta Jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Share via
Copy link
Powered by Social Snap